16 Agusta 2021 - 15:08
Labanon: Mutane 28 Sun Mutu Sakamakon Fashewar Wata Tankar Mai Arewacin Кasar

Ma’aikatar lafiya ta ƙasar Labanon ta sanar da cewa alal aƙalla mutane 28 sun mutu wasu da dama kuma sun sami raunuka sakamakon fashewar wata tankar mai a yankin Akkar da ke arewacin ƙasar.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran AFP ya jiyo wani babban jami’in Ma’aikatar lafiyar ta Labanon, Reda Moussawi yana tabbatar da wannan labarin inda ya ce a halin yanzu adadin mutanen da suka rasa rayukan na su sun kai mutane 28 sakamakon fashewar tankar man a kauyen Talil a safiyar yau Lahadi.

Tun da fari dai ƙungiyar agaji ta Red Cross ta ƙasar Labanon ɗin ta ce mutane 20 ne suka mutu kana wasu 79 kuma suka sami raunuka.

Wasu rahotanni sun ce lamarin ya faru ne bayan da jami’an tsaro suka ƙwace wata tankar mai da masu sayar da mai ta bayan fage suka ɓoye cike da man fetur, to a yayin da suke raba wa mutane mai ɗin ne tankar ta fashe.

Кasar Labanon ɗin tana fuskantar tsananin ƙarancin makamashi da ya haɗa da man fetur, gas da kalanzir da sauran lamarin da ya sanya al’ummar ƙasar cikin tsaka mai wuya cikin ‘yan watannin baya-bayan nan.

342/